Labarai
Tinubu ya taya Soludo murna bisa sake lashe zaɓen gwamnan Anambra

Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya murna ga gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo bisa samun nasarar sake lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar, inda ya yaba wa mutanen jihar bisa gudanar da zaɓen cikin lumana.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a kafofin sada zumuna Tinubu ya kuma yaba wa ƙoƙarin da ya ce, hukumar zaɓen Najeriya INEC ta yi.
Shugaban ya ce ya ziyarci jihar a watan Mayun da ya gabata domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan ya yi, waɗanda ya bayyana da ayyuka masu muhimmanci da nagarta
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya kuma yaba wa Soludo bisa yadda yake gudanar a mulki mai kyau domin ciyar da jihar Anambra gaba. Sannan ya yi kira gare shi da ya janyo abokan hamayyarsa kusa domin haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ciyar da jihar gaba.
You must be logged in to post a comment Login