Labarai
Tinubu zai dauki matakin biyan kananan hukumomin kasar nan kai tsaye

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin ƙasar su yi biyayya ga umarnin kotun ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ƴancin tafiyar da kuɗaɗen su.
Shugaban ya ce rashin aiwatar da wannan tsari ka iya tilasta masa zartar da wata doka da za ta ba shi ikon aikewa ƙananan hukumomin kuɗinsu kai tsaye daga asusun kwamitin rabon arzikin tarayya.
Tinubu ya yi wannan gargaɗin ne a wajen taron majalisar zartarwar jam’iyyar APC karo na 15 da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.
“Ina matuƙar mutumta ku ne kawai, a matsayin gwamnonina. Amma idan ba ku fara aiwatar da wannan umarni daki-daki ba. za ku ga abin da zai faru,” in ji Tinubu. .
A ranar 11 ga watan Yulin 2024 kotun ƙoli ta bayar da hukuncin da ya tabbatar da buƙatar gwamnatin tarayya ta bai wa ƙananan hukumomin Najeriya ƴancin tafiyar da kuɗaɗensu.
Dukkan alƙalan kotun bakwai sun amince da hukuncin cewa riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi ke yi ya saɓawa tanadin kundin mulkin ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login