Connect with us

Labarai

Ina goyon bayan bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai – Jonathan

Published

on

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bukaci majalisun dokokin tarayya da su gaggauta ayyana dokar da za ta bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai.

 

A cewar tsohon shugaban kasar kamata ya yi dokar ta bai wa kananan hukumomin ‘yancin neman kudaden shiga da kansu.

 

Goodluck Jonathan ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke zantawa da shugabannin kungiyar ma’aikatan kananan  hukumomi ta kasa NULGE wadanda suka kai masa ziyara gidansa da ke garin Otuoke a jihar Bayelsa.

 

Tsohon shugaban kasar ya ce da shi dan majalisa ne da abin da zai yi shine neman goyon bayan abokansa don bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai.

 

A cewar Jonathan al’ummar da ke yankunan kananan hukumomi suna da ‘yancin amfana da dukiyarsu, a don haka  ba daidai bane dukiyoyinsu  su rika makalewa a jihohi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!