Labaran Wasanni
Tokyo 2020: Rukunin farko na tawagar Najeriya zai tashi zuwa Tokyo
Rukunin farko na tawagar ‘yan wasan da za su wakilci Najeriya a gasar Olympics ta 2020 da za a gudanar a Tokyo, za su tashi daga Najeriya zuwa kasar Japan.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da jami’in yada labaran ma’aikatar wasanni ya rabawa manema labarai.
Tawagar ‘yan wasan za su tashi daga Najeriya ta jirgin Ethiopian Airline a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Najeriya dai za ta fafata a wasanni tara wadanda za a fara daga 23 ga watan Yuli zuwa 8 ga Agusta, yayin da guragu za su fafata a wasanni hudu daga ranar 24 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumbar 2021.
A halin yanzu, hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya (WA) ta tabbatar da cewa Najeriya za fafata wasanni 13 ne a gasar da za a gudanar a birnin Tokyo dake kasar Japan.
You must be logged in to post a comment Login