Ƙetare
Trump ya tsawaita wa’adin kai wa Iran hari zuwa makwanni 2

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya amince da dakatar da kai hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu, domin ba da damar kammala tattaunawar zaman lafiya.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin Truth Social, Trump ya ce ya yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa da Firaministan Shehbaz Sharif da kuma babban hafsan soji Asim Munir na ƙasar Pakistan.
Trump ya ce Iran ta gabatar da shawarwari guda goma, waɗanda ya ce za su iya zama tubali wajen kulla yarjejeniya, ciki har da buɗe mashigar Hormuz cikin gaggawa.
Sai dai ya jaddada cewa wannan tsagaita wuta na ɗan lokaci zai ba ɓangarorin damar kammala tattaunawa da cimma matsaya ta ƙarshe.
You must be logged in to post a comment Login