Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaftar muhalli – An yankewa Yan garuwa tarar naira dari biyar

Published

on

An yankewa Yan garuwa tarar naira dari biyar biyar sakamakon karya dokar tsaftar muhalli.

Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta gargadi masu sana’ar sayar da ruwa a kura da su kiyaye karya dokar tsaftar karshen wata wata.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin da yake zagayen duba yadda mutane ke bin dokar a Asabar din nan.

“Mun lura a yanzu masu sana’ar garuwa su ne suka fi karya mana doka a duk karshen wata a don haka za mu fara aiwatar da hukunci a kan su”

“Dokar tsaftar muhalli bata daukewa kowanne dan jihar Kano ba, a don haka ana bukatar kowa ya zauna a gida ya tsaftace gidan sa da cikin unguwa”

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, za su samar da dokar da za ta fara hukunta Yan garuwar don tabbatar da ganin kowa yabi doka.

“Muna sahalewa masu uzuri na musamman su fita ranar tsaftar muhalli amma ba za mu zuba idanu kowa ya rika yawo a lokacin da doka bata amince ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!