Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An ci tarar wasu kamfanoni bisa karya dokar tsaftar muhalli

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta yankewa wasu kamfanoni biyu tarar naira dubu dari biyar kowannen su.

Kamfanonin biyu sun hadar da JK company da GP Tank da ke rukunin masana’antu na sharada.

Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli karkashin mai shari’a Aminu Muhammad Gabari ce ta yanke hukuncin.

Hukuncin ya biyo bayan yadda aka samu kamfanonin biyu sun bude suna ci gaba da kasuwancin su daidai lokacin da ake gudanar da tsaftar muhalli na karshen wata.

Tuni dai kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya bada umarnin aikewa da kamfanonin biyu takardar rufewa har sai sun cika ka’idojin da aka gindaya musu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!