Labarai
Tsaftar muhalli: Gwamnatin Kano ta yi sammacin shugabannin kasuwar Rimi
Gwamnatin jihar Kano ta yi sammacin shugabannin kasuwar Rimi sakamakon rashin tsaftar muhalli.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya yi sammacin na su, lokacin da ya ke duban tsaftar muhalli na karshen kowanne wata a kasuwar.
Wannan dai ya biyo bayan yadda kwamishinan muhallin ya tarar da kasuwar cikin kazanta, a hannu guda kuma wata kungiyar da ke zaman kan ta mai rajin tsaftar muhalli na gudanar da aikin gyaran magudanan ruwa a kasuwar ba tare da gudunmawar shugabannin kasuwar ba.
“Mun zo kasuwar Rimi mun kuma tarar da Kungiya na gudanar da tsaftace kasuwar, sai dai abin takaici babu shugabannin kasuwar ko guda daya a wajen don nuna goyon bayan su da gudunmawar su, duk da an sanar da su za a yi aikin a wannan rana” a cewar Getso.
Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya kuma ce kowacce shekara gwamnatin Kano na fitar da kudi wajen gyara kasuwar amma rashin mayar da hankali na shugabannin kasuwar na haifar da koma baya.
“Kwarai abinda shugabannin kasuwar Rimi suka aikata abin Allah wadai ne da takaici, a don haka muna bukatar shugabannin kasuwar da su zo gaban mu don jin ba’asi” inji kwamishinan.
Dakta Kabiru Getso ya ce, gwamnati za ta ci gaba da daukan matakan ladabtarwa kan masu kin tsaftace muhalli.
You must be logged in to post a comment Login