Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yanzu-yanzu: Gwamnatin jihar Kano ta ci tarar miliyan biyu ga yan kasuwar Singa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano yankawa shugabannin ‘yan kasuwar Singa tarar kudi miliyan 2.

Tarar tasu dai, ta biyo bayan rashin tsaftace kasuwar da suka yi na karshen wata nan.

Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bada umarnin cin tararsu, karkashin kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli.

Ya ce, an yanke hukuncin ne karkashin sashi na 27 a dokar kula da tsaftar muhalli ta shekarar 2016.

Tuni dai an aike musu da sammaci tare da bukatar su biya tarar kudi naira miliyan 2.

Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, wannan izina ce ga dukkan wata kasuwa da ta karya dokar tsaftar muhalli.

Kotun tafi da gidanka karkashin mai shari’a Auwal  Yusuf Sulaiman ta bai wa shugabannin kasuwar wa’adin kwanaki uku da su tsaftace kasuwar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!