Labarai
Tsaftar muhalli: Kotu ta rufe wasu banɗakunan haya a Kano
Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli ta rufe wasu banɗakunan haya guda biyu a kasuwar Ƴankaba saboda rashin tsafta.
Kotun ta yanke hukuncin ne ƙarƙashin mai Shari’a Auwal Yusuf lokacin da kwamitin duban tsaftar muhalli ya kai ziyara kasuwar da safiyar ranar Asabar ɗinnan.
Da yake ƙarin haske kan rufe banɗakunan kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, matakin ya biyo bayan yadda aka samu banɗakunan cikin rashin tsafta a daidai lokacin da ake gudanar da tsaftar muhalli na ƙarshen wata.
Dakta Getso ya ce “Mun samu banɗakunan kasuwar guda biyu cikin ƙazanta da rashin tsafta abin takaici, a don haka kotun tafi da gidanka ta basu takarda kuma ta rufe banɗakunan har sai sun gurfana gaban ta”.
“Zai iya yiwuwa bayan an hukunta shugabannin da ke kula da banɗakunan kuma a ci su tara bisa laifin da suka aikata kamar yadda dokokin tsaftar muhalli suka tanadar”.
Tsaftar muhallin na watan Disamba ya zo adaidai lokacin da ake bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, kuma an yi masa take da “Duban tsaftar muhalli na musamman kuma na ƙarshen shekara”.
Kwamitin duban tsaftar muhallin ya kuma ziyarci wajen zubar da shara da ke ofishin Wakilin Kudu da na makarantar firamare ta Jarkasa don ganin yadda ake gudanar da ayyukan.
You must be logged in to post a comment Login