Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsafta: Gwamnatin Kano ta rufe kamfanoni bisa karya dokar muhalli

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wasu kamfanoni biyu saboda karya dokar tsaftar muhalli.

An rufe kamfanonin biyu Nina Plastic da Prosper Plastic da ke sarrafa robobi a unguwar Challawa saboda karya dokar tsaftar muhalli na ƙarshen wata.

Hakan ya faru ne yayin rangadin da Kwamishinan muhalli na Kano Dr. Kabiru Ibrahim Getso ya jagoranta da safiyar Asabar.

Kwamishinan ya ce, an hukunta kamfanonin ne ƙarƙashin kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli.

Da ya ke, yanke hukunci mai shari’a Auwal Yusuf Sulaiman ya yanke musu hukuncin rufewa nan take, tare da biyan tarar Naira dubu dari biyar kowannensu kafin kammala bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!