Labarai
Tsagaita dokar Zirga-Zirga: Bankuna sun cika makil a Kano
Yau ne Gwamnatin jihar Kano ta ware don al’umma su fita dan gudanar da siyayya a kasuwanni bayan da dokar hana fita ta sati daya ta cika, a wani mataki na magance yaduwar cutar Corona.
Dalilin sassauta dokar a yau ya sanya aka samu cinkoson jama’a a bakin na’urorin cirar kudi ta ATM, mutane kan dauki lokaci da dama kafin su ciri kudi, bayan haka kuma an samu cinkoson ababen hawa a titunan na birnin Kano.
Haka zalika Freedom Radiyo ta zaga wasu daga cikin bankunan dake kan Titin Isyaka Rabi’u dana singa da Sharada da kantin kwari da kuma gidan zoo inda nan ma ta tarar da taron jama’a a bakin na’urar ta ATM.
Freedom Radiyo ta zanta da wasu daga cikin mutanan da suka zo cirar kudin kan ko me yasa basu shiga cikin banki ba don karbar kudin nasu ko a samu ragin cin koson jama’ar sai suka ce an hana mutane shiga cikin bankunan wanda sai dai su tsaya a na’urar ta ATM.
Wasu daga cikin mutanen Freedom din ta zanta dasu sun nuna takaicinsu kan karancin kudi da ake fuskanta a irin wannan lokaci.
You must be logged in to post a comment Login