Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Ƴan bindiga sun sace mutane 8 a Neja

Published

on

A ƙalla mutane takwas ne ƴan bindiga suka sace a wani sabon hari da suka kai wa Fulanin Agwan a Kwakwashi ta jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na daren Talata, kamar yadda wani mazaunin yankin, Joseph Ake ya shaida.

A cewar sa ƴan bindigar sun yi ta harbe -harbe lokacin da suka shiga ƙauyen, tare da yin awon gaba da mutane tara, sai dai ɗaya daga ciki ya kuɓuta daga hannun su bayan ya samu munanan raunuka.

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami’in hulda da jama’a Abiodun Wasiu, sai dai bai bayar da cikakken bayani kan harin ba, inda ya ce, an tura jami’an tsaro don aikin bincike da ceto su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!