Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Fasa kwauri: Mun kama haramtattun kaya na miliyan sittin a Katsina – Kwastam

Published

on

Hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa Kwastam ta cafke wasu haramtattun kaya da aka shiga da su ƙasar nan da kudin su ya kai naira miliyan sittin a Katsina.

Kwastam ta ce, daga ranar 8 ga watan Yuli zuwa 3 ga watan Agustan 2021 ta cafke wasu motoci 13 da buhun shinkafa ƴar waje 314 da aka shigo da su.

Shugaban hukumar shiyyar Katsina Dalha Wada ne ya bayyana hakan a Kaduna, yayin da yake yiwa manema labarai ƙarin bayani kan nasarar da suka samu a tsakanin wannan lokaci.

Dalha Wada ya ce, “Mun kama wasu motoci da aka shigo da su ta ɓarauniyar hanya da kuɗin su ya kai naira miliyan arba’in da biyu da dubu ɗari ɗaya, sai shinkafa yar waje da kuɗin ta ya kai naira miliyan bakwai da dubu ɗari biyar”.

Shugaban hukumar ya bayyana sauran kayan da cewa, “akwai Mai na jarka da muka kama shi ma an shigo da shi da kuɗin sa ya kai sama da naira miliyan biyar, yayin da taliyar kwali ƴar waje kuɗin ta ya kai sama da dubu ɗari tara da sittin da ɗaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!