Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: An hana cinikin fili da gidaje a Minjibir

Published

on

Karamar hukumar Minjibir ta haramta sayar da gidaje da ba da hayar su.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Sale Ado Minjibir ne ya bayyana hakan yayin wani taro da ya kira na masu rike da mukaman gargajiya da malamai har ma da dillalai.

Ganawar ta su ta mayar da hankali kan tattauna hanyoyin da za a magance matsalar tsaro a karamar hukumar, ganin yadda lamarin ke ci gaba da yawaita a fadin kasar nan.

Alhaji Sale Ado Minjibir ya ce, za su yi hadin guiwa da jami’an tsaro wajen bai wa mafarauta horo kan sha’anin tsaro, tare da tura su zuwa iyakokin karamar hukumar don kyautata tsaro.

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!