Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Tsaro: An kama mutane biyu da ake zargi da kashe dan sintiri a Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatarda yin nasarar kama wasu matasa biyu da ake zargi da laifin kashe wani dan kugiyar sintiri a gidansa dake karamar hukumar Kiru a nan Kano.

A cewar rundunar matasan sun haura gidan dan kungiyar sintirin mai suna Ibrahim Shu’aibu a ranar ashirin da tara ga watan da ya gabata a cikin dare dauke da makamai suka kuma harbeshi.

Daga cikin wadanda ake zargin akwai Abdulganiyyu Gambo dake Kauyen Kariya a Kiru sai Muhammad Sani dake Hayin Gwarmai a karamar Hukumar Bebeji.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ta Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, matasan da aka kama sun tabbatar da aikata laifin da ake zarginsu dashi kuma sun kwashe sama da shekaru takwas suna garkuwa da mutane da kuma satar Shanun jama’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!