Labarai
Tsaro: Ana ci gaba da yin sulhu da ‘yan bindiga a Katsina

Ƙananan hukumomin Malumfashi da Funtua da Bakori sun bi sahun wasu takwarorinsu da suka yi sulhu da ƴanbindigar a jihar da ke fama da matsalar tsaro.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ƴanbindiga masu kai hare-hare a ƙauyuka da garuruwan jihar da kashe mutane da sace wasu domin neman kuɗin fansa.
An gudanar da zaman sulhun ne a garin Kakumi da ke yankin ƙaramar hukumar Bakori, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta bayyana.
Taron sulhun ya samu halartar shugabannin alumomin yankunan da wakilan ƴanbindigar.
A baya-bayan nan ana ta samun ƙaruwar hare hare a ƙananan hukumomin Katsina inda a ka rungumar sulhu a wani mataki na magance matsalar tsaron jihar.
You must be logged in to post a comment Login