Labarai
Tsaro: Gwamnonin yankin Kudu maso gabashin Najeriya sun kafa kungiyar sintiri
Gwamnonin yankin Kudu maso gabashin kasar nan sun bi sahun takwarorinsu na Kudu maso yammaci wajen kafa kungiyar sintiri da za ta kare yankin daga ayyukan bata-gari.
Shugaban kungiyar gwamnonin yankin kuma gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi ne ya karanta takardar bayan taro ga manema labarai a birnin Owerri na jihar Imo.
“Mun bijiro da tsarin ne domin kyautata harkokin tsaro a yankin namu,” inji Dave Umahi.
Umahi ya ce kungiyarsu ta yi allawadai da harin da wasu bata-gari suka kai a ofishin ‘yan sanda da gidan gyaran hali a Jihar ta Imo, inda suka hallaka wasu mutane ciki har da jami’an tsaro sannan suka saki daurarrun gidan.
A baya dai gwamnonin Kudu maso yammacin kasar nan sun sanyawa kungiyar sintirin ta yankinsu sunan Amotekun, yayin da ita kuwa ta kudu maso gabashi ta sanyawa ta ta sunan Ebube Agu.
You must be logged in to post a comment Login