Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ofishin Babban Akanta ya fitar da kudi naira biliyan 666 ba bisa ka’ida ba – Majalisa

Published

on

Majlissar Dattijai ta ce ofishin babban akanta na kasa ya fitar da kusan naira biliyan 666 daga asusun albarkatun kasa ba bisa ka’ida ba.

Wannan dai na zuwa ne ta cikin rahoton da kwamitin harkokin kudi na majalisar ya gabatar kan binciken kudi da ya gudanar tsawon watanni 6.

Kwamitin ya ce, ofishin babban akantan ya bada basukan kudaden ne ga wasu hukumomin gwamnati tsakanin shekara 2004 zuwa 2015 ba bisa ka’ida ba.

Majalisar dattijan ta ce, yanzu haka dai kwamitin ya fara bincikar kudaden da hukumomin gwamnatin tarayya suka kashe daga 2015 zuwa 2018, kamar yadda rahoton Ofishin babban Odita na kasa ya fitar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!