Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro – Sojojin Najeriya sun hallaka yan ta’adda uku

Published

on

Sojojin Najeriya da ke aiki a garin Sabon Birni da ke kan iyaka da jihar Sakkwato sun kashe wasu ‘yan bindiga uku tare da kwato makamai.

Samamen ya biyo bayan samun sahihan bayanan cewa ‘yan bindiga suna jigilar makamai a kafa daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya.

A cewar Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima, Sojojin da ke yankin sun yi kwanton bauna a kan hanyar wani kauye tare da kashe maharan guda 3.

A cewar sa kayayyakin da aka kwato sun hada da bama-bamai da babura da kuma bindiga kirar AK47 da kayan adon kunne da kuma alburusai daban-daban.

Sai dai tuni Babban Hafsan sojin Najeriya Manjo Janar Faruk Yahaya ya yabawa kokarin da sojojin suka yi sannan ya bukace su da su ci gaba da aiki ta hanyar mamaye dukkanin haramtattun hanyoyi da ke kan iyakokin Jamhuriyar Nijar don dakile ayyakan bata gari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!