Labarai
Tsofaffin dalibai: Za mu tallafa wa jami’ar Bayero
Kungiyar tsofaffin daliban tsohuwar kwalejin Abdullahi Bayero a nan Kano da aka canja zuwa Jami’ar Bayero, sun sha alwashin gudanar da wasu ayyuka na tallafawa jami’ar tare da karrama wasu malamai da suka koyar da su a wancan lokaci.
Mataimakin shugaban tsare-tsare na kungiyar tsofaffin daliban, Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa ne ya bayyana haka bayan kammala shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan Freedom Rediyo da ya mayar da hankali kan taron tsofaffin daliban makarantar kafin a canja sunanta zuwa Jami’ar Bayero ,da ake shirin gudanarwa ranar Asabar mai zuwa.
Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa wanda shi ne Dan Masanin Dutse, ya ce taron zai tattaro sauran tsofaffin daliban da ke raye da nufin tayar da tsimin zumuncin su tun suna dalibai a makarantar.
Daya daga cikin tsofaffin dalibai mata na makarantar a wancan lokaci da ta kasance cikin shirin, Hajiya Uwani Yahya cewa ta yi sun shirya gudanar da taron ne don karfafa zumunci tsakanin su inda ake da shi tare da kulla sabo dadewa baa hadu ba.
Haka kuma, sun yi fatan samun nasarar gudanar da taron da kuma kyakkyawar manufar da ta sanya aka shirya gudanar da shi.