Labarai
Tsohon shugaban hukumar INEC ya karyata zarginsa na runbon adana bayanai
Tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa INEC farfesa Attahiru Jega ya karyata rade-raden da ake yadawa kan akwai runbon adana bayanai a yayin da yake jagorantar hukumar.
Farfesa Attahiru Jega ya bayyana hakan ne a yayin da aike da wasikar kartakwana ga jaridar PREMIUM TIMES bayan da suka tuntube shi kan zargin da wasu ke yi cewa akwai runbon adana bayanai a yayin dake rike da hukumar wajen tattara bayanan zabe, kuma ake ta yadawa a kafafan sada zumunata.
Sai dai farfesan ya ce wannan zancen kitsa shi kawai aka yi shi bashi da masaniya kan wannan batun.
Rahotanni sun bayyana cewar akwanan nan ne ake ta yada kalamai da aka ambato tsohon shugaban hukumar INEC Farfesa Attahiru Jega na cewa hukumar ta INEC ta mallaki runbon adana bayanai tun a zamanin sa kuma yana aiki kawo yanzu.
Attahiru Jega dai shi ne ya gaji Maurice Iwu wanda ya rike hukumar ta INCE zuwa shekara ta 2015.