Kiwon Lafiya
Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya bukaci zaman lafiya a zabe mai karatowa
Tsohon shugaban kasar nan Olusegun Obasanjo ya bukaci al’ummar kasar nan da su ci gaba da kokari wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar nan musamman ma a wannan lokaci da babban zaben kasar nan ke karatowa.
Olusegun Obasanjo ya gargadi al’ummar kasar nan da cewar matukar aka samu farkewar rashin zaman lafiya lokacin zabe to kada ace daga, All.. ne illa iya ka al’ummar kasa ne suka kirkiri hakan.
Tsohon shugaban kasar na wadannan kalamai ne ya yin da yake mika sako bikin kirsimate ga al’ummar kasar nan a garin Abeokutan jihar Ogun.
Ya kuma jaddada fatan sa na ganin shekarar 2019 ta zama abin alfahari ga al’ummar kasar nan ta hanyar gudanar da sahihin zabe da wanzar da zaman lafiya. Tsohon shugaban kasar cikin sakon nasa ya ce a halin yanzu dai, kasar nan na bukatar hadin kan juna da kuma yin hakuri da juna, a cewar sa ta hakan ne kawai za a iya samun zaman lafiya mai dorewa