Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

TUC tan janye zanga-zangar lumuna da ta shirye

Published

on

Hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa TUC ta dage zanga-zangar da ta shirya yi zuwa ranar 28 ga watan satumbar da muke ciki.

Shugaban kungiyar reshen jihar Lagos Mr Gbenga Ekundayo ne ya bayyana hakan ga manema labaraia jiya Talata.

Ya ce, dage zanga zangar ya biyo bayan cimma yarjejeniya yin zanga-zangar tare da kungiyar kwadago ta kasa NLC wadda a jiya ta sanar da ranar da zata gudanar da zanga zangar a kasa baki daya.

Ekundayo, ya ce yin zanga zangar ya biyo bayan rashin cimma yarjejenioya tsakaninj kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya sakamakon Karin farashin man fetur da wutar lantarki da aka yi a baya bayan nan.

A don haka kungiyar ta amince ta hade dage zanga zangar da kungiyar kwadago wadda zata gudanar a ranar 28 ga watan satumbar da muke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!