Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

UCL: Manchester City tayi nasara akan Athletico Madrid a gasar

Published

on

Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester City da ke kasar Ingila tayi nasarar doke Athletico Madrid da ci daya da nema a gasar cin kofin zakarun turai.

Fafatawar da ta gudana a filin Etihad na kasar Ingila, kwallon da dan wasa De Bruyne ya zura jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Wasan dai shi ne zagaye na dab dana kusa da karshe wato Quarter Final a gasar ta kakar wasannin shekarar 2021/2022.

Athletico Madrid dai na karkashin jagorancin Diego Simeone da ya kai tawagar wasan karshe har sau uku a baya amma basuyi nasara ba.

Yayinda Pep Guardiola ke jagorantar City da take yunkurin lashe gasar a karo na farko a tarihi tin lokacin da aka kafa kungiyar.

Zuwa yanzu dai za a jira buga wasa zagaye na biyu a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid a mako mai zuwa, domin sanin kungiyar da zata kai wasan kusa da karshe a gasar da ake fafatawa.

A daya wasan da aka buga a gasar Liverpool tayi nasara akan Bendica da ci 3 da 2 a fafatawar da suka gudanar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!