Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Umaru Musa ‘yar Adua ya cika shekaru 13 da rasuwa

Published

on

A ranar 5 ga watan Mayun shekarata 2010 Allah ya yiwa Umaru Musa ‘Yar Adua rasuwa a fadar gwamnati da ke Abuja watanni biyu bayan komowarsa gida daga kasar Saudiya inda yake jinya.

An haifi Umar Musa Yar’adua a ranar 16 ga watan Agustan shekara ta 1951 a cikin birnin Katsina da ke arewacin Najeriya.Mahaifinsa ya kasance tsohon ministan birnin Lagos na farko a jamhuriya ta farko, kuma kafin rasuwar sa shi ne Matawallen Katsina, sarautar da shi marigayin Umaru Musa ‘Yar’adua ya gada daga wajen mahaifinsa wato Musa Yar’adua. Akwai dan uwansa babban yayan sa watau Shehu Musa Yar’adua, wanda shi ma shahararren ɗan siyasa ne a kasar Najeriya; kuma shi ya kafa jam’iyyar “PDM” People’s Democratic Movement, Shehu Musa Yar’adua ya rasu a gidan yari a shekarar 1997.

Marigayi Umaru Musa Yar’aduwa ya fara makarantar Firamarensa ne a Rafukka ne a shekara ta 1958, kafin a mayar da shi makarantar sakandare ta kwana da ke karamar hukumar Dutsin ma a shekara ta 1962. Ya kuma halarci kwalejin gwamnati da ke Keffi daga shekarata 1965 zuwa shekarata 1969. Sai ya wuce kwalejin Barewa a shekarata 1971, inda ya samu takardar shedar karatunsa ta HSC, daga bisa ni ya kuma halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria daga shekarata 1972 zuwa shekara ta 1978 inda ya samu takardar shedar dagari akan kimiyyar haɗa sinadirai wato Chemistry da Koyarwa, ya kuma samu babban digiri duk dai akan kimiyyar hada sinadarai Marigayin yayi bautar ƙasarsa ne a Jihar Lagos inda ya koyar a makarantar Holy Trinity daga shekarar 1975 zuwa shekara ta 1976.

Daga bisani ya shiga harkar koyarwa, daga nan kuma ya koma bangaren noma, daga.

Bayan ya shiga siyasa ne kuma, ya samu sabani da mahaifinsa, wanda a wancan lokacin yake mataimakin shugaban Jam’iyar NPN, inda shi kuma ya zama wakili a jam’iyar PRP ta Malam Aminu Kano mai adawa da NPN. A lokacin da Janar Babangida ya kaɗa gangar siyasa ya zama sakataren jam’iyar SDP a jihar ta Katsina kuma ɗan takararta na gwamna, amma kuma ɗan takarar jam’iyar NRC na wancan lokaci Malam Saidu Barda ya kada shi a zaben. To sai dai duk da haka bai hakuri ba inda a shekara ta 1999 Malam Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya tsaya takarar muƙamin gwamnan jihar ta Katsina kuma ya samu nasara a ƙarƙashin jam’iyar PDP.

A shekarar 2007 Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya zama ɗan takarar muƙamin shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP bayan ya samu taimakon tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo  ya zama shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2007, wannan ya bashi daman sanya rigar siyasa na koli a shekarar.

To sai dai rashin lafiya da tsohon shugaban ya yi fama da ita, ta sanya bai samu sukunin gudanar da harkokin mulki kamar yadda ya yi fata ba, daga bisani kuma Allah  yayi masa rasuwa sanadiyar rashin lafiya da ya daɗe yana jinya, ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekarata 2010 a fadar gwamnati da ke Abuja watanni biyu bayan komowarsa gida daga kasar Saudiya inda yake jinya. Inda ya bar ‘yan’uwansa da matan Aure guda biyu Hajiya Turai ‘Yar adua tare da ‘ya’ya bakwai da ya haifa da ita da suka haɗa da mata biyar, da maza biyu. Haka kuma yana da wasu ‘ya’ya biyu maza da matarsa ta biyu Hajiya Hauwa Umar Rdda.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!