Manyan Labarai
UNICEF ta yi alkawarin cigaba da tallafawa Najeriya
Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya yi alkawarin cigaba da tallafawa Najeriya ta bangarori da dama da suka hada da: harkokin Ilimi da lafiya da muhalli da kuma manufofin gwamnatin da ke neman kyautata rayuwar al’ummar kasar.
Babban jami’in asusun na UNICEF mai kula da jihohin, Kano da Katsina da kuma Jigawa, Mista Maulid Warfa ne ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai wa gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari.
Babban jami’in na UNICEF, ya shaidawa gwamnan cewa shi dan asalin kasar Habasha ne aka yi masa sauyin wajen aiki daga kasar Iraki zuwa Najeriya, ya ce wadannan matsaloli na daga cikin batutuwa da za su mayar da hankali wajen bayar da gudunmawarsu.
Ya ce asusun na UNICEF zai cigaba da aiki tare da gwamnatin jihar Katsina wajen bunkasa harkokin ilimi da lafiya.
Da ya ke mai da jawabi gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bukaci asusun na UNICEF da ya kara zage damtse wajen inganta ayyukan da za su tallafawa cigaban al’umma.