Connect with us

Labarai

Commonwealth:ta nada Ngozi Okonjo Iwela a matsayin babbar jami’a sakatariyar kungiyar

Published

on

Kungiyar kasashen rainon ingila, Commonwealth, ta nada tsohuwar ministar kudi Misis Ngozi Okonjo Iwela, a matsayin babban jami’a a sakatariyar kungiyar.

 

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da Kakakin kungiyar Ferfesa Ben Maloney ya fitar tare da sanya hannu.

 

Sanarwar ta ce, an zabe ta ne sakamakon cancanta ta, bisa la’akari da gudunmowar da ta bayar a lokacin mulki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

 

Sanarwar ta kara da cewa, tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Kiribati Mista Anote Tong ne ya jagoranci matsayin tun daga shekara ta 2003 zuwa 2016.

 

Kungiyar ta ce tuni dai ta kaddamar da wani kwamiti da zai fara bibiyar wadda za ta  zama sarauniya a kungiyar

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,589 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!