Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Uwargida ta gayyaci al’umma shagalin bikin yi mata kishiya

Published

on

Uwargida ta gayyaci al’umma shagalin bikin yi mata kishiya .

Awanna lokaci da ake fama da fadace -fadacen mata kishiyoyi ,kai har ma da yunkurin kisa duk a dalilin aure ko yin kishiya da ya yi kamari sai ga wani lamari ya bullo na abu mai kamar wuya wai Gurguwa da auren nesa.

Wata mata mai suna Sa’adat Hassan, ta fito fili a shafin ta na dandalin sada zumunta na Facebook tana gayyatar al’umma zuwa shagalin bikin Karin aure da mijinta zai yi.

A sanarwar Sa’adat Hassan, ta sanar dacewa za’ayi shagalin bikin ranar 11 ga watan Afrilun wata mai kamawa, don haka tana gayyatar kowa da kowa, tare da fatan Allah ya albarkaci auren ya basu zaman lafiya.

Lamarin dai ya baiwa, al’umma da dama mamaki, inda a martanin da aka dinga mayar mata , an yaba da juriyar ta, da kuma addu’a da tayi, tare da taya ta murna.

Bugu da kari jama’a da dama sunyi mata addu’ar Allah yasa abokiyar zaman nata da za’a aura ta zama mai hali na hakuri irin nata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!