Kasuwanci
VAT Crisis: Gwamnatin jihar Rivers ta shigar da kara a kotun koli
Gwamnatin jihar Rivers ta shigar da kara a kotun koli don kalubalantar hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan takaddamar karbar harajin kayayyaki na VAT, tsakanin jihar da hukumar tattara kudaden haraji ta kasa (FIRS).
Babban Lauya mai kare hakkin bil’adama, Emmanuel Ukala SAN tare da wasu manyan lauyoyi uku ne su ka shigar da daukaka karar zuwa kotun kolin.
Atoni Janar din jihar ta Rivers ne mai daukaka karar yayin da FIRS da kuma Atoni Janar na kasa, Abubakar Malami SAN su ka kasance masu shigar da kara.
Gwamnatin jihar ta shaida wa kotun kolin rashin amincewar ta da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar Juma’a 10 ga watan Satumbar 2021 inda ta umarci bangarorin biyu da kowa ya tsaya a matsayin sa.
Kotun ta ce abin da hukuncin kotun daukaka kara ke nufi shi ne ta mayar da kowane bangare a matsayin sa kafin wata Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal ta ba wa gwamnatin Jihar ’yancin karbar kudin harajin VAT, maimakon FIRS a ranar 9 ga watan Agusta.
You must be logged in to post a comment Login