Connect with us

Kaduna

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta tsige shugaban masu rinjaye

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta tsige shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Mohammed Inuwa da ke wakiltar karamar hukumar Doka da Gabasawa.

Hukuncin hakan ya biyo bayan rashin samun magoya baya da yayi daga mambobin zauren majalisar.

Mambobin majalisar 17 na jam’iyyar APC sun kaɗa kuri’ar amincewa da tsige shi daga mukamin shugabancin masu rinjaye na majalisar.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar, shugaban kwamitin yada labarai Tanimu Musa ya ce, an tsige shi sakamakon rashin samun tabbaci a kan sa.
Sai dai ya ce, za a sanar da sabon shugaban bada jimawa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!