Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Victor Osimhen bazai buga wasanni biyu ba a gasar Seria A

Published

on

Hukumar kwallon kafar kasar Italiya ta dakatar da dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Napoli Victor Osimhen, dake buga gasar Seria A ta kasar wasanni biyu.

Victor Osimhen dan asalin Najeriya dake wasa a kungiyar kwallon kafa ta kasar Super Eagles ya samu katin kora daga wasa wato Jankati a wasan da kungiyar sa ta Napoli ta lallasa Venezia da ci 2-0 a ranar Lahadi 22 ga watan Agustan 2021.

Dan wasan ya samu jankatin ne a minti na 23 da fara wasan.

Wanna dai shine karo na farko da tsohon dan wasan Wolfsburg da  Lille ya karbi katin kora a wasannin da yake fafatawa daban-daban.

Yanzu dai Osimhen ba zai buga wasannin da kungiyar sa ta Napoli za ta yi ba da  Genoa da kuma Juventus a ranakun 29 ga Agusta da kuma 11 ga Satumba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!