Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Federico Valverde ya sabunta kwantaragin sa da Real Madrid

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sabunta kwantaragin dan wasan tsakiyarta, Federico Valverde na tsawon shekaru 2, inda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2027.

Valverde mai shekaru  23 wanda kwantaraginsa ke shirin karewa a shekarar 2025 kawo yanzu zai ci gabada wasa a Real Madrid.

Dan wasa Valverde ya koma Real Madrid a watan Janairun shekarar 2016 daga karamar kungiyar ta  Castilla, kafin ya je zaman aro zuwa Deportivo La Coruna da kawo yanzu ke buga wasa a filin  Estadio Santiago Bernabeu.

Dan wasan dai ya fara fafata wasa tun a lokacin tsohowan mai horar da kungiyar Julen Lopetegui.

Valverde ya buga wasanni 104 a  Real Madrid tare da ‘yan wasa irin su Casemiro mai shekaru  (29) da Toni Kroos mai shekaru (32) da kuma dan wasa Luka Modric mai shekaru 35.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!