Labaran Kano
Wadansu magidanta sun karbi Musulunci a garin Sumaila
A yankin Sumaila dake garin Kano hukumar Shari’ar Musulunci tare da hadin gwiwar kwamitin yada addinin musulinci dake karamar hukumar Tudun Wada karkashin jagorancin Malam Nasiru Alhassan sun musuluntar da wani magidanci tare da matarsa dake gundumar Gani dake Sumaila a yammacin Talata .
Yayin da suke karbar Kalmar shahada sun nuna farin cikin su da godiya ga Allah [ SWT ] dangane da fahimtar gaskiya tare da kuma kama tafarkin tsira, kamar yadda Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam ya koyar.
Mai gidan kamar yadda ya bayyana yace duk abin da aka ce rabon mutum ne daga ubangiji sai mutum ya tarar da shiriyar Allah madaukakin Sarki.
Ya kara bayyana cewa, duk mutumin da yazo Duniya rayuwa ya kamata ya san makomar sa bayan mutuwar sa.
Magidacin ya nemi a san ya masa sunan Marigayi Sheikh Jaafar yayin da matar sa ma ta nemi a sa mata suna Hafsatu.
Shima a nasa bangaran, Malam Nasiru Alhasan yace ya shafe tsawon shekaru yana yin da’awar shigowar su musulunci kafin Allah ya fahimtar dasu .
Malam Nasiru yace akalla shekara 13 yana Da’awah amma kiran bai isa zuciyar su ba sai a yanzu.
Ya kara bayyana irin mu’amalantar su da yayi ta abinci da tufafin su da ma Addinin su duk saboda ribato zukatansu na tsawon shekara goma sha uku.