Coronavirus
Wanda ya kamu da Corona a Jigawa yana nan da ransa
Gwamnatin jihar Jigawa ta musanta rade-radin da ake yawa cewa, wanda aka samu dauke da cutar Corona a jihar ya mutu.
Kwamishinan Lafiya na jihar kuma shugaban kwamatin dakile cutar a jihar Dakta Abba Zakari Umar ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radiyo game da rade-radin da ake yadawa na mutuwar wanda aka samu dauke da cutar a jihar.
Dakta Abba Zakari Umar ya kuma ce zuwa yanzu wanda aka samu dauke da cutar an killaceshi a daya daga cikin cibiyar killace masu dauke da cutar da gwamnatin jihar ta tanada dake Garin Dutse babban birnin jihar ta Jigawa.
Ya kuma ce wanda aka samu dauke da cutar ba dan asalin jihar ta Jigawa bane, dan jihar Enugu ne wanda ke gudanar da kasuwancinsa a jihar ta Jigawa.
Covid-19: Gwamnatin jihar Jigawa ta samar da gadaje sama da 300
Yanzu-yanzu: Coronavirus ta shiga Jigawa
Abba Zakari Umar ya ce adon haka duk wanda aka samu dauke da cutar dake zaune a jihar ko a wacce jiha yake gwamnati zata bashi kulawar da ta kamata wajen killaceshi da bashi magunguna.
A cewar sa “duk wani mutum dan Najeriya suna kallon sa ne dai-dai yake da dan asalin jihar ta Jigwa domin kuwa duk kasa daya ake ba tare da nuna banbancin yare ko addini ba”.
A Lahadin nan ne dai gwamman jihar ta Jigawa Alhaji Badaru Abubakar Talamiz ya bayar da sanarwar rufe garin Kazaure inda aka samu bullar cutar na tsawon mako guda domin ganin an dakileta ba tare da ta shiga wasu sassa na jihar ba.
You must be logged in to post a comment Login