Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wani hatsarin mota ya jikkata mutane 20 wasu da dama sun mutu a ƙaramar hukumar Kura

Published

on

Ana fargabar mutuwar mutane da dama yayin da 20 suka jikkata, a wani hatsarin mota da ya afku a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura anan Kano.

Haɗarin dai ya afkune bayan da wata mota kirar Golf ta yi ƙoƙarin wuce wasu manyan motocin dakon kaya, lamarin da ya sanya direban motar ya gaza cin birki.

Wannan ne ya sanya motocin suka yi taho mugama a ƙoƙarin da suka yi na kaucewa mai ƙaramar motar, nan ta ke motocin guda 3 suka kama da wuta.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa mai ƙaramar motar ne ke gudun wuce sa’a kuma shi ne musamabbabin faruwar lamarin.

Ko da Freedom Radio ta tuntuɓoi hukumar kashe gobara ta jihar Kano, mai magana da yawun ta Saminu Yusif ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Sai dai ya ce, tuni jami’an su suka isa wajen da lamarin ya faru, kuma da zarar sun dawo za su yi ƙarin bayani.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!