Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Wani magidanci me mata hudu yayi yaji sakamakon   cin zarafi da matansa ke yi

Published

on

A yayinda a ke bikin ranar cin zarafin mata ta Duniya, wani magidanci ya bayyana yadda matan sa ke cin zarafinsa.

A yanzu haka wannan magidanci me suna Malam Rabi’u dake wannan ikirari ya bayyana yadda matan sa su hudu ke cin zara finsa.

Yace yayi  yaji ne tun daga garin Katsina Ala, da ke a jahar Benue zuwa wajen yar uwarsa dake a nan Kano, me suna Asma’u Muhammad.

Wakiliyar mu Zulaihat Yusif Aji ta zanta da wannan magidanci, wanda ya bayyana mata yadda wannan al amari ya kasance.

Mal Rabi’u ya kara da cewa wannan al’amari na “Yajin maza” ba sabon abu bane a wajen maza.

Yace bacin rai da yake samu a wajen matansa ko wace rana ya sa shi wannan yaji.

Daga karshe ‘’yar uwar  magidancin Asma’u Muhammad wacce ya gudo wajen da take zaune a Kano, ta bayyana yadda al’amarin ya faru inda ta ce zasu mai dashi daga baya, amma se matan sun gyara kuskuransu .

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!