Connect with us

Labarai

Wani miji ya fasawa matar sa ido

Published

on

Shi dai wannan mutum, matar shi tayi karar shine zuwa hukumar kare hakkin dan adam dake cikin Kano, domin kuwa tace yana yawan dokan ta, yakan yi naushi da mari harma yayi tsalle akan ruwan cikin ta.

Tace a yayin da yake dukanta ne sai ya sa me ta a idon ta wanda hakan takai da idon nata ya samu matsala.

Matar ta kara da cewa wannan bashi ne na farko ba da takai karar shi ba hasali ma har rantsuwa ya taba yi da alkur’ani cewa ba zai sake dokan ta ba amman hakan bai hana ya cigaba da halin sa ba.

Matar ta nemi da hukuma ta shiga tsakanin ta da wannan Mijin nata da sauran ‘ya’yan da suke tsakanin ta dashi.

Mata da miji sun sha duka a hannun wanda ake zargi da kwartanci

Cin zarafin mata ya yi yawa a Kano –Farfesa Hadiza Galadanci

Tilas a magance cin zarafin mata- Mai dakin Sarkin Kano.

Suma daga bangaren hukumar kare hakin dan adam sun tofa albarkacin bakin su akan wannan lamari kuma sun nuna rashin jin dadin su inda sukace zasu nemi wannan mutum da ake zargi domin ayi bincike a gane gaskiyar batun.

Freedom Radio sun samu damar zantawa da wannan mutumin da ake zargi inda suka tambayi shi akan zargin da matarsa ta ke mishi shi kuwa yace ba gaskiya bane shi bai san maganar ba.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,262 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!