Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A bamu aiki ko mu koma bara-Makafin Kano

Published

on

Kungiyar makafi ta jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga lumana a nan Kano.

Zanga-zanagar ta fara ne daga ofishin ma’aikata zuwa majalisar dokoki na  nan Kano ya dagana zuwa hukumar ilimin bai daya USBEB.

Makasudun wannan zanaga-zangar shi ne yadda shugaban hukumar ilimin bai daya Dan Lami Hayyu yaki sanya sunayen makafi cikin malaman da za’a dauka.

Su dai makafin na ikirarin cewar Dan lami Hayyu ba zasu iya koyar ba, kasancewar ana bukatar kwararru ne.

Sama da mutum 2,000 ne suka amfana da kayan masarufi na azumi da Hajiya Halima Shekarau ta raba

Matasa sun yi zanga-zanga kan aikin Titin Five Kilometer

Niger- Matasa sun yi zanga-zanga dangane da lalatattun tituna a Minna

Sai dai wakilin mu Yusuf Ali Abdullah ya tuntubi shugaban hukumar ilimin bai daya yana mai cewa baya gari yana jihar Katsina don gudunar da aiki, amma ya ce da zarar ya sami sarari zai neme mu, amma  kawo lokacin da muke hada muku wannan rahoton bai ce komai ba.

Akan haka ne wakilin mu ya tuntubi ofishin shugaban ma’aikata na jihar Kano Dr, Kabiru Shehu, shi ma aka ce yana ganawa da sababin kwamishinoni, ba zai samu sukunin tattaunawa da mu.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!