Labaran Kano
Cin zarafin mata ya yi yawa a Kano –Farfesa Hadiza Galadanci
Kungiyar tallafawa mata da sana’o’in dogaro da kai wato Women’s Organization for Relief and Empowerment, (WORE) wadda mai dakin sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II, Hajiya Maryam Muhammadu Sanusi II take jagoranta, ta gabatar da wani taro mai taken “Rikicin dake faruwa tsakanin iyali, da hanyoyin da za’a magance su”
A yayin taron an tattauna matsalolin da ‘ya’ya mata ke shiga a gidajen Aurensu wanda sanadiyar hakan yakan sanya su shiga harkar shaye-shaye, da ciwon damuwa.
Farfesa Hadiza Galadanci na daya daga cikin wadanda suka gabatar da makala a wajen taron, ta bayyana cewa a matsayinta na likita tana karbar matsalolin cin zarafi na cikin gida babu adadi, wadanda suka hadar da duka,mari, da sauran su.
Wakiliyar mu Samira Sa’ad Zakirai ta rawaito mana cewa,taron ya samu halartar manyan mata daga sassa daban-daban na kasar nan wadanda suka hadar da Farfesa Rukayya El-rufa’I, da Sanata Baraka Sani, da Malama Halima Shitu, da mai dakin gwamnan jihar Sakoto Hajiya Mairo Maryam Aminu Waziri Tambuwal, da kuma wakiliyar (Yaya Susan to Plss need it)mai dakin gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufa’I, sai Dakta Hauwa Abdullahi, da Farfesa Aisha Tofa, da Maryam Ahmad Sabo MNI, da kuma Malama Ummukulsum Kassim.
Rubutu masu alaka:
Maza sunfi bada muhimmanci ga sunnar karin aure –Halima Shitu