Kaduna
Hatsarin kwale-kwale yayi sanadiyyar mutuwar Mutane 29 a a Jahar Niger

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, ta tabbatar da sake aukuwar wani sabon hatsarin kwale-kwale wanda yayi sanadiyyar mutwar akalla mutane 29 a gabar kogin Malale da ke a karamar hukumar Borgu a Jihar.
Darakta Janar na hukumar Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Baba yace, Kwale-kwalen mai dauke da fasinjoji 90 yatashi ne daga Tugan Sule inda ya nufi Dugga domin zuwa wata ta’aziyya.
Yace cikin wadanda suka mutu har da mata da kananan yara, kuma zuwa yanzu an gano gawarwaki 29, yayin da aka ceto mutum 50 da ransu, sai kuma wasu mutum biyu da haryanzu ake ta kokarin lalubosu.
You must be logged in to post a comment Login