Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mutane 18 sun rasu sanadiyyar hatsarin kwale-kwale

Published

on

A kalla mutane 18 ne suka rasa rayuwakansu sakamakon hatsarin kwale-kwale a Kogin Buji da ke karamar hukumar Itas Gadau.

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar ta su,ta cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar DSP Ahmed Muhammed Wakil ya fitar, ta ce 16 daga cikin wadanda suka rasa rayukansu kananan yara ne.

 

Sai dai yace, masu aikin ceto sun samu nasarar ceto mutane biyar wadanda biyu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.

 

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan jirgin kwale-kwalen yana dauke ne da manoma ashirin da uku lokacin da ya yi hatsarin.

 

Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da:  Abdulraham Shehu; Suwaiba Yusuf, Saude Abdulkarim, Fatima Maigari, Zuwaira Maigari, Hari Maigari, Hussaina Maigari, Ummani Abdulkarim da kuma Halima Saminu.

 

Sauran sune: Najaatu Hamza, Nura Abdullahi, Yahuza Abdullahi, Hafsa Abdullahi, Sadiya Hashimu, Khadija Alhassan, Amina Idris, Kaltime Hudu da kuma Furaira Malam Magaji.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!