Kimiyya
Wasu ɗaliban Kano sun shiga jerin masana kimiyya da fasaha a duniya
Ɗalibai ƴan asalin jihar Kano biyar sun shiga jerin sunayen waɗanda
suka yi fice wajen ilimin kimiyya da fasaha a duniya.
Sunayen ɗaliban da a ka wallafa a watan Agustan shekarar da ta gabata ta 2021, wanda wasu tawagar masu bincike ƙarƙashin jagorancin Farfesa John Loannidis na Jami’ar Stanford da ke California a Amurka suka fitar.
To sai dai guda uku daga cikin ɗaliban sun samu tagomashin ne cikin waɗanda tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya tura karatu zuwa ƙasashen waje domin yin digiri na biyu.
Da ga cikin su dai akwai ‘yan Kwankwasiyya Scholars uku wadanda a ka fi kafa hujja da su, da suka haɗar da Dakta Aliyu Isa Aliyu da Dakta Tukur Abdulkadir Sulaiman sai Dakta Abdullahi Yusuf.
Sauran biyun kuwa sune Farfesa Abdurrazaq Garba Habib da Farfesa Umar Ibrahim Gaya.
Aƙalla dai masana a fannin kimiyya da fasaha sama da miliyan takwas ne masu bincike a Jami’ar ta Standard suka yi nazari a kan su, kuma suka fitar da fitattu mutum dubu ɗari da a kafi amfanuwa da bayanansu ta ɓangaren kimiyya da fasaha.
Wannan ne ya kawo adadin mutum 120 daga nan gida Najeriya waɗanda suka samu damar shiga wannan sahu.
A shekara ta 2012 ne dai gwamna Kwankwaso ya ɗauki nauyin karatun ɗaliban zuwa ƙasashen ƙetare domin yin digiri na biyu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke garin Irbid.
Wanda kawo yanzu uku daga ciki sun samu muƙamin Dakta a sashen Ilimin Lissafi na Jami’ar Tarayya da ke Dutsen Jihar Jigawa.
You must be logged in to post a comment Login