Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wasu mata sun yi zanga-zanga a Kano kan sace ‘ya’yan su

Published

on

Wasu mata da aka sace musu ‘ya’ya sun gudanar da zanga-zangar lumana zuwa ofishin hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano don nuna takaicinsu kan batan yaran nasu.

Matan wadanda suka fara zanga-zangar tun daga unguwar ‘Yan Kaba sun zuwa ofishin na anti corruption sun ce sun yi hakan ne don janyo hankalin gwamnatin Kano game da mawuyacin halin da suka shiga sanadiyar batan yaran nasu.

Daya daga cikin masu zanga-zangar mai suna Malama Lubabatu Abdullahi ta ce sun damu matuka game da yadda batun ceto sauran yaran nasu ke neman shirirucewa.

Sai dai ya zuwa wannan lokaci ba abar matan shiga harabar ofishin ba, inda masu kula da ofishin suka sanar dasu cewa babu wani babban jamii da zai sauraresu saboda dukkanninsu suna ofishin wucin gadi na hukumar dake Goron Dutse

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!