Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zamu dakatar da fasfon wadanda suka ki amincewa da gwajin Corona – Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya tace ba dadewa ba zata dakatar da fasfon masu shiga da fice cikin kasar nan da suka ki yarda da ayi musu gwajin cutar Corona.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana haka ga manema labarai a birnin tarayya Abuja, in da ya kara dacewar gwamnatin zata fitar da sunayen mutane 100 da suka kaucewa ka’idojin gwajin  a jaridun kasar nan.

Boss Mustapha, yace gwamnatin zata dau matakin dakatar da fasfon masu shige da fice cikin kasar nan daga farkon shekara mai kamawa zuwa  watan Yuni  don ya zama izina da gargadi ga masu niyyar kin  bin ka’idojin.

Sakataren gwamnatin ya tabbatar da cewar gwamnatin ta kammala shirye shirye don samar da rigakafin cutar ga al’ummar kasar nan tare da ware wasu sabbin dakunan gwaje gwaje don fuskanta tare da dakile cutar a a karo na biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!