Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mata uku sun mutu sakamakon konewa sakamakon konewa a hatsarin motar bas a Kano

Published

on

Mutane 3 ne suka mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a wutar da ta tashi cikin wata motar haya kirar Lita Hayis, a kan titin state road daura da kwalejin Takanikal dake birnin Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar SFS Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan ta cikin wani sakon murya da ya aikowa freedom radio a daren jiya.

 

SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya ce, motar ta taso ne daga karamar hukumar Ajingi da nufin zuwa kasuwar kofar Wambai’.

‘Hadarin dai ya faru ne sakamakon cirewar tayar motar ta baya, da hakan ya kaisu ga hadari’.’

Ya kuma ce ‘an samu ceto mutum 13 daga cikin 16, yayin da wasu mata 3 da bayan an samu nasarar ceto su daga motar daga bisani suka rasu.

Cikin wadanda suka rasu akwai Zee 9 Babaji da Surayya Umar da kuma dayar da ba’’a san sunanta ba, yayin da sauran 13 kuma suka samu raunuka na kuna a jikin su’.

Rahoton: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!