Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yan sanda a Kano sun kama matasa 2 bisa zargin kashe Budurwa

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, ta kama wasu matasa biyu da take zarginsu da laifin hallaka wata budurwa Theressa Yakubu yar shekara 20, ta hanyar shake mata wuya da zani, bayan sun yi kokarin zubar mata da ciki a karamar hukumar Bebeji.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai da yammacin jiya Talata.

Ya ce, rundunar ta samu rahoton samun Budurwa a kwance cikin mawuyacin hali a garin Ana Dariya da ke karamar hukumar Bebeji ranar 28 ga watan jiya na Maris inda yan sanda suka garzaya da ita zuwa asibiti garin Tiga, wanda a nan aka tabbatar da mutuwarta.

SP Kiyawa ya ce, matashiyar mai suna Taressa Yakubu tana dauke da juna biyu wanda ake zargin saurayinta ne yayi mata, wanda kuma a kokarin zubar da cikin ne suka hallakata ta hanyar shake mata wuya da mayafinta.

Ibrahim Philibus, mai shekaru 20 shi ne saurayin Theressa kuma wanda ake zargi da hallaka ta, a tambayoyin da rundunar yan sanda ta yi masa ya amsa laifin tare da cewa shi ne ya kashe ta tare da taimakon abokinsa.

Haka kuma ya ƙara da cewa, ya hallaka ta ne ya hanyar daure mata wuya da mayafinta bayan da ya dakko ta a kan babur da nufin kai ta wurin da za a zubar mata da cikin wata biyu da Phillip din ya yi mata.

Gebril Edah mai shekaru 25, shi ne abokina saurayin Theressa wanda kuma ake zargin tare suka hada kai wajen kashe ta, shi ma ya amsa laifin yin hadin kai wajen kashe ta inda ya ce, shi ne ya rike hannun Theressa yayin da abokin nasa ya shake mata wuya har ta mutu.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa, yanzu haka rundunar ta kusa kammala bincike domin gurfanar da su a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!