Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wasu matasa sun Kona babur din adai-daita sahun masu kwacen waya bayan sun musu dukan tsiya a Kano

Published

on

Wasu matasa a yankin Kabuga dake karamar hukumar Gwale a Jihar Kano sun kone wani baburin adai-daita sahu da ake zargin na masu kwacen waya ne.

Wani shaidar gani da ido ya bayyanawa freedom Radio cewa tun da fari matasan sai da suka lakadawa masu kwacen wayar duka lokacin da suka taho suna kwacewa mutane wayoyinsu sannan suka damka su a hannun jami’an tsaro daga bisani kuma suka cinnawa adai-daita sahun wuta.

Wannan dai na zuwa ne adaidai lokacin da rundunar Yan sanda Jihar Kano ke cewa tana iya bakin ko karinta wajen kawo karshen kwacen waya ta hanyar kama barayin tare da gurfanar dasu gaban shari’a.

Yayin da a hannu guda al’ummar Jihar suke ganin hukuncin da ake yiwa masu kwacen wayar yayi rauni, da yasa kullum matsalar take Kara habaka a fadin Jihar.

Rahoton: Bashir Sharfadi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!