Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Daliban Sudan a Nijeriya na fargabar halin da karatunsu zai iya shiga na rashin madafa.

Published

on

Dubban daliban Nijeriya ne da su ka dawo daga kasar Sudan bayan barkewar yaki a Sudan din ke cigaba da fargabar halin da  karatun su zai iya shiga na tangal-tangal bayan tsaiko da suka samu, sakamakon tahowa ba shiri.

Daliban dai sun ce a yanzu haka sun bar karatun nasu ne ba tare da sanin ranar komawarsu Makarantar ba, dalilin yakin da ake gwabzawa a Sudan din, da ba ranar dainawa.

Daliban da suke ajin karshen a matakin digri din sune suka fi nuna damuwarsu, biyo bayan rashin mafitar da karatun nasu zai iya fuskanta.

Su ma iyayen wadan nan dalibai sun nuna damuwa kan zaman ‘Ya ‘yan na su a gida musamman wadanda karatun su ya yi nisa ko ma su ke shirin kammalawa.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin yawancin daliban sunje karatun ne, bayan gwamnati da dai-daikun al’umma sun dauki nauyinsu.

Hakan tasa suke kira ga gwamnati data samar musu mafita, don Kar karatun nasu ya tashi a banza.

Sai dai wata majiya mai karfi ta nuna cewa a yanzu haka gwamnati na Kan tattauna hanyar da zata bi, don ganin ta samarwa wadannan daliban da abin ya shafa mafita.

Rahoton: Alameen Sulaiman

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!