Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wata cuta da ba a kai ga gano asalinta ba ta hallaka mutane 6 a Kano

Published

on

Wata cuta da ba a kai ga gano asalinta ta ba ta yi sanadiyyar mutuwar mutane shida bayan da mutane sama da arba’in suka kamu da ita a yankin Kyarmawa dake garin Kantse cikin karamar hukumar Dawakin Kudu.

Wakilin Dagacin garin na Kantse Malam Muhammad Abubakar ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da wakilinmu Abubakar Tijjani Rabi’u, dangane da samun bullar cutar da aka yi a garin na Kyarmawa.

Dangane da hakan ne ya sa wakilin na mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya yi kokarin jin ta bakin ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, inda ya tuntubi daraktan sashen dakile yaduwar cututtuka masu yaduwa na ma’aikatar Dr Ashiru Rajab ta wayar tarho.

Sai dai har zuwa wannan lokaci bai amsa kiran na mu ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana da muka tura masa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!